MU

MU YI HATTARA DA TCHIANI

 

Idan ba rainin wayo ba, bai kamata a ce shugaban kasa shi zai yi irin maganganun da Tchiani ya yi ba. Ya ce Najeriya na hada kai da Faransa ana horas da yanta’adda don su durkusar da Nijer. Ya ce akwai sansanin da Faransawa suka kafa a dajin Baga. Ya ce Lakurawa na cikin wadanda ake amfani da su. Ya ce… Maganganu dai ga su nan. Kan ka ce kwabo yan Arewarmu sun karba suna ta yadawa a matsayin gaskiya don wauta ko don hamayya. 

 

In yana fa’da ne saboda ya samu karbuwa wajen mutanen kasarsa, chan ta matse musu. Amma ya kasance mu ‘yan Najeriya muna kula shi, muna gaskata duk abinda ya fada, ina ga babu hikima a ciki.

 

Na farko dai Tchiani ba zai hana mu bai wa yan Nijer mafaka ba. Da ma rabin yan Nijer a Najeriya suke. Su suka cika mana dazuzzuka da kiwo, da noma, da kasuwanninmu, musamman shagunan gefen hanya da ba sa kan ka’ida, da aikin gadi, mun ba su wurare sun gina gidaje, da zama yanakasa dss duk da sunan yan’uwa. 

 

Shi kuma Tchiani juyin mulki ya yi ba zabensa aka yi ba. Don haka idan wata kasar ECOWAS ta ba da mafaka ga masu adawa da shi, wannan ba laifi ba ne. Ba mu da wata yarjejjeniya da Nijar da ta bukaci mu hana su kamar yadda ba mu hana sauran yan Nijer zama a Najeriya ba, da takardu ko babu.

 

Hasali ma, ai ya ce ba ruwansa da ECOWAS wacce Najeriya ke jagoranta. To mu yan ECOWAS ne. Yá janye sojojinsa daga rundunar hadin gwiwa tsakanin Najeriya, Tchad da Cameroon wacce take yaki da ta’addanci. Ya ce Mali da Burkina ne abokan huldarsa. So, sai ya je su ukun su kadai su yaki Lakurawan da ISWAP da Buzaye da sauran yantawaye da suka jima a kasarsu. Kar ya jawo Najeriya a ciki. Lakurawa dai daga Nijer suka fara shigo mana a 2016.

 

Batun Faranshi kuwa, tsakaninsu ne, ba abinda ya shafe mu. Mu ba yan Nijer ba ne. Yan Najeriya ne. Muna da iko mu yi kowace irin hulda da Faranshi idan akwai maslaha gare mu. Ai mun hana wa Amurkawa sansani, Nijer ta ba su. Don haka ina ruwanta in muna hulda da Faranshi ko ma za mu ba Faranshi sansani?

 

Balle ma mun san iyakar dangantakarmu da kowace kasa. Tunda sojojinmu suka hana Obasanjo kafa sansanin Amurkawa, ina ga wata tsohuwar shajini mai suna Faransa?

 

Ya kamata Tchiani ya fahimci mutuncin Nijer da muke gani saboda yan’uwantaka bai ba shi damar daukanmu bayin ra’ayinsa ba. Ba zai yi amfani da haka ba don ya rika wasa da hankalinmu. Ya tsaya ya fuskanci Faranshi da yanta’addansa masu yawa, kala kala, da kuma sabaninsa da Benin. Ba ka yanke hulda da makwabtanka sannan ka dawo kana mita. In zai hada kai da mu don samun zaman lafiya ya hada. In ya zabi ya ware, to ya je chan. Ci naka in ci nawa ba rowa ba ne, mugun zama ne.

 

NSA Nuhu Ribadu ya nemi yanjarida da su karade Najeriya kaf, har da dajin Baga din, su ga ko akwai wani sansanin Faransa. In har Nijer ko yanjarida ba su kawo mana hujja ba, to ya tabbata dole mu fara hattara da Tchiani saboda yana amfani da mutuncin da ke tsakaninmu da Nijer don cimma burinsa na siyasa da rena mana wayo.

 

Wata shidan da ECOWAS ta bayar za su kare a watan June. Nijer dole ya zabi hulda da mu yan ECOWAS ko da Mali da Burkina. Duk zabin da ta yi, muna shirye mu yi hulda da ita ta yadda ECOWAS za ta tsai da shawara. 

 

Nijer yan’uwanmu ne amma Tchiani ba shugabanmu ba ne. Fakad.

 

Dr. Aliyu U. Tilde

26 Disamba 2024

SIMILAR STORIES

Subscribe to our Newsletter

Advertisement

Poll